Yau Litinin ne ma’aikatan sufurin jiragen saman ƙasar nan suka fara yajin aikin kwanaki biyu, domin neman a kyautata musu yanayin aiki da kuma wasu kuɗaɗe da suke bin gwamnati.
Tun a ranar Juma’ar da ta gabata ne, ma’aikatan sufurin suka sha alwashin tsunduma yajin aikin karo nan a biyu da suke daukar irin matakin a cikin shekarar nan.
Ma’aikatan sun hada da matuka jirgin sama, da injiniyoyi da masu kula da zirga-zirgar jiragen saman a sararin samaniya, da dai sauran ma’aikatan filayen jiragen,
Sun ce za su kaurace wa aiki ne a ranakun yau Litinin da gobe Talata bisa la’akari da basukan da suke bi, da kuma matakin gwamnati na rusa ofisoshin wasu hukumomin sufurin jiragen sama a Legas domin fadada filin jirgin saman birnin.
Ɓangaren sufurin jiragen saman ƙasar nan na fuskantar matsaloli da suka hada da rashin ingancin kayayyakin aiki a wasu filayen jirage, da karancin mai da ke taƙaita zirga-zirgarsu a cikin gida da kuma rashin isassun kudaden kasashen waje wanda ya sa kamfanonin jirage na kasa da kasa biyan wani kaso na kudaden da suke samu daga sayar da tikitinsu.