• Home  
  • Majalisa Ta Amince A Kirƙiro Jihohi Shida A Najeriya
- Babban Labari - Labarai

Majalisa Ta Amince A Kirƙiro Jihohi Shida A Najeriya

Kwamitin haɗin gwiwa na majalisar dattawa da ta wakilan Najeriya kan yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar garambawul ya amince da a ƙirƙiro jihohi guda shida. Wannan na cikin matsayar da aka cimmawa a ƙarshen taron ƙara wa juna sani na kwana biyu, wanda mataimakin majalisar dattawa Sanata Barau I. Jibrin da mataimakin shugaban majalisar […]

Kwamitin haɗin gwiwa na majalisar dattawa da ta wakilan Najeriya kan yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar garambawul ya amince da a ƙirƙiro jihohi guda shida.

Wannan na cikin matsayar da aka cimmawa a ƙarshen taron ƙara wa juna sani na kwana biyu, wanda mataimakin majalisar dattawa Sanata Barau I. Jibrin da mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu suka jagoranta a jihar Legas.

Kwamitin ya tattauna ne kan buƙatu guda 69, ciki har da buƙatar ƙirƙirar jihohi 55 da buƙatar a ƙirƙirar ƙananan hukumomin 278 kamar yadda jaridar Daily Trust mai zaman kanta ta ruwaito.

A game da buƙatar ƙirƙirar jihohi 55 da aka gabatar a ranar Asabar, kwamitin ya amince da ƙirƙirar jihohi guda shida a duk shiyoyin ƙasar guda shida.

Idan aka amince da ƙirƙirar sababbin jihohi, Najeriya za ta zama tana da jihohi 42 ke nan.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai