Za a miƙa ƴan Najeriya da ake zargi damfara zuwa Amurka
Za a miƙa wasu ƴan Najeriya shida da hukumomin Amurka ke nema ruwa a jallo bisa zargin damfarar sama da mata 100 ta hanyar zambar soyayya a intanet daga Afirka ta Kudu zuwa Amurka a yau. Masu gabatar da ƙara a Amurka sun ce ana tuhumar mutanen da laifin damfara da kuma halatta kuɗaɗen haram. […]









