Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana tashin hankalin da ke faruwa a Sudan a matsayin abin takaici, inda ya gargadi taron Majalisar a jiya Talata cewa yakin na iya yaduwa zuwa wasu kasashen yankin.
A halin da ake ciki wani jirgin ruwa dauke da fararen hula 1,687 daga kasashe fiye da 50 da suka tsere daga rikicin Sudan ya isa kasar Saudiyya, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen kasar ta bayyana, wanda shi ne aikin ceto mafi girma da masarautar Gulf ta yi a halin yanzu. Sanarwar ta ce, kawo yanzu an kwashe mutane 2,148 zuwa masarautar daga Sudan, ciki har da baki fiye da 2,000.