Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa a Najeriya ta soki ƙudurin da Majalisar wakilan ƙasar nan ta gabatar da ke neman tilasta wa likitoci yin aikin shekaru biyar kafin samun lasisi fara yin aiki a matsayin likitoci a ƙasar nan.
A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar bayan taron gaggawa na shuwagabanninta, ta nuna adawarta game da wannan ƙuduri.
Sanarwar ta ce ƙungiyar ta yi mamaki game da wanda ya gabatar da ƙudurin Honourable Ganiyu Johnson.
Haka kuma kungiyar ta bayyana damuwarta kan rashin biyan albashi da ta ce gwamnatin tarraya ba ta yi wa wasu daga cikin mambobinta ba, a yayin da wa’adin gwamnatin ke zuwa ƙarshe.
Ƙungiyar ta ce ta damu kan yunƙurin majalisar wakilan na tilasta wa likitoci abin da ta kira da ”karin zangon shekara biyar bayan karatun digiri” kafin a ba su lasisi, ko a bar su su fita zuwa ƙasashen waje idan suna da sha’awar yin hakan.
Ƙungiyar ta kuma nuna damuwa kan sake duba albashin mambobinta da ta ce gwamnatin tarayya ta gaza yi, duk kuwa da irin tarin alƙawuran da kungiyar ta ce gwamnatin ta sha yi musu.