Wasu mutum biyu da ake zargin ɗaliban jami’a ne a Jihar Bayelsa sun mutu bayan wata mota ƙirar tifa ta murƙushe su lokacin da suke kan babur mai ƙafa uku a kan hanyar Tombia zuwa Ammassoma.
Daily Trust ta samu rahoton cewa haɗarin wanda ya afku a ranar Talata, ya kuma sa wasu fasinjojin da ke cikin babur ɗin sun samu munanan raunuka.
A cewar wasu mazauna yankin, haɗarin ya afku ne a kusa da wani lanƙwasa mai haɗarin gaske a kan babbar hanyar, sakamakon rashin kyan hanyar da kuma gudun wuce ƙima.
Wani ɗan kasuwa mai suna Godspower Okolo, ya shaida wa manema labarai cewa direban tifa ɗin yana tafiya da sauri, kuma a lokacin da ya yi yunƙurin karkatar da motar abin ya citura.
- Ɗalibin Jami’a Ya Kashe Kansa Bayan Faɗuwa Jarabawa
- Majalisar Kano Ta Dakatar Da Shugaban Karamar Hukuma Kan Zargin Almundahana
Ya ce, “Keke (Babur mai ƙafa uku) ba ta da damar kaucewa hatsarin, domin kuwa tifa ɗin ta riga ta yi kusa da shi, mun yi ta ƙorafin yadda direbobin manyan motocin dakon kaya suke yi a wannan hanyar tsawon shekaru, amma babu abin da ya canza.
“Haɗarin ya sa babur ɗin ya lalace ba tare da an gane fasinjojin cikin ba, wasu masu jinƙai ne suka garzaya wurin da lamarin ya faru, inda suka kwashe waɗanda suka tsira daga haɗarin tare da kai waɗanda suka jikkata zuwa cibiyar lafiya ta tarayya da ke Yenagoa, daga baya aka kwashe gawarwakin waɗanda suka mutu zuwa ɗakin ajiye gawa na kusa.
“Wannan lamarin ya sake sabunta kiraye-kirayen a tsaurara matakan tsaro, ya kamata hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) da rundunar ’yan sanda ta jihar su ƙara yin sintiri, da ɓullo da na’urorin hana gudu, da kuma gudanar da binciken ababan hawa kan manyan motoci,” in ji shi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Bayelsa, DSP Musa Muhammad, ya tabbatar da faruwar haɗarin, inda ya ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin haɗarin motar.

