A jiya Juma’a ne ma’aikatan wannan gidan Radiyo da Talabijin na MUHASA TVR suka je ta’aziyya ga iyalan marigayi Hassan Mohammed Lamin a gidansu na Gandu da ke unguwar ƙoƙi a cikin ƙwaryar birnin Kano.
An kai wannan ziyara ne a bisa jagorancin Mataimakiyar shugaban wannan gida Hajiya Aishatu Sule wacce ta yi addu’ar Allah ya jiƙan marigayin da kuma ba shi gidan Aljanna Firdaus.
Sannan ta taya iyalan marigayin alhinin wannan babban rashi da aka yi tare da addu’ar samun ƙarfin guiwar jure wannan babban rashin.
Ɗan uwa kuma abokin tagwaitakar marigayin, Malam Hussaini Muhammed Lamin, wanda shi ne shugaban Sashen Kasuwanci na Muhasa TVR, a yayin da yake karɓar gaisuwar ta’aziyyar, ya yi addu’ar Allah ya ba da ladan zumunci da kuma miƙa godiyarsa ga hukumar gudanarwar gidan.
A ranar 13 ga watan Afrilu, ya yi dai- dai da 22 ga watan Ramadan, 1444, Malam Hassan Muhammed Lamin, ya rasu, bayan gajeriyar jinya kuma yana da shekaru 60.
Kafin rasuwarsa Hassan Lamin ɗan kasuwa ne wanda kasuwancinsa ya kai shi ƙasashe daban-daban, sai kuma harkar addini da aka san shi da shi.
Marigayin ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya 13 da ‘yan uwa maza da mata waɗanda a cikinsu ne har da Mallam Hussaini Lamin na nan gidan Muhasa TVR.
A ƙarshe muna addu’ar Allah ya jiƙan waɗanda suka riga mu gidan gaskiya, Ya kuma kyautata namu zuwan, amin.