• Home  
  • Nafi’u ya gargaɗi Atiku ya daina sukar Tinubu da sunan ADC
- Babban Labari

Nafi’u ya gargaɗi Atiku ya daina sukar Tinubu da sunan ADC

Jam’iyyar ADC ɓangaren Nafiu Bala Gombe ta yi Allah-wadai da yadda ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar tsagin David Mark, Atiku Abubakar yake amfani da suna da logon jam’iyyar wajen yin sojan gona ba bisa ƙa’ida ba. Cikin wata sanarwa da Nafi’u Bala ya sanya wa hannu a yau 31 ga watan Agusta, ya ce […]

Jam’iyyar ADC ɓangaren Nafiu Bala Gombe ta yi Allah-wadai da yadda ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar tsagin David Mark, Atiku Abubakar yake amfani da suna da logon jam’iyyar wajen yin sojan gona ba bisa ƙa’ida ba.

Cikin wata sanarwa da Nafi’u Bala ya sanya wa hannu a yau 31 ga watan Agusta, ya ce jam’iyyarsu ba za ta lamunci a riƙa amfani da sunanta ba wajen ƙarya da cin mutunci Najeriya ba a idon duniya, inda ta ce hakan cin amanar ƙasa ne da kuma taɓa ƙimarta.

Sanarwar ta ƙara da cewa bai kamata a riƙa aibanta gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu haka kurin, duk da cewa ko wannan ɗan ƙasa na da ‘yancin samun kariya a dokance, amma ya kamata a yi komai bisa doron abubuwan da dokokin Najeriya suka tanada.

Kwamtin amintattu na jam’iyyar in ji sanarwar ya ce shigar da ƙara a wata ƙasa da Alhaji Atiku Abubakar ya yi kan shugaban Najeriya rashin kishin ƙasa ne, abin kunya ne, kuma babban cin fuska ga tsaron ƙasa da muradun Najeriya. Wannan ƙoƙari ne na mayar da siyasar cikin gida zuwa batun duniya domin biyan buƙatun kai.

“Muna sanar da Alhaji Atiku Abubakar da ya daina nan take bayyana kansa ko magana a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC. Duk wani ƙoƙarin sake haɗa sunan jam’iyyar da rikicin siyasarsa ko ayyukan da za su jawo wa Najeriya baƙin jini a idon duniya zai fuskanci sakamako na doka da siyasa”.

Ya ƙara da cewa Muna sanar da Alhaji Atiku Abubakar da ya daina nan take bayyana kansa ko magana a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC. Duk wani ƙoƙarin sake haɗa sunan jam’iyyar da rikicin siyasarsa ko ayyukan da za su jawo wa Najeriya baƙin jini a idon duniya zai fuskanci sakamako na doka da siyasa.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai