Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Najeriya NAHCON, ta ce ta samo mafita, dangane da batun ƙarin kudi dala 250 da aka samu na tikitin jiragen sama na aikin hajjin bana.
A yanzu an sami rangwamen dala hamsin da biyar, kuma maniyyata za su cika dala 100 daga cikin kuɗin guzurinsu, yayin da ake sa ran samun rangwamen ragowar dala goma sha bakwai daga ɓangaren kamfanonin jiragen saman.
A wata tattaunawa da manema labarai, kwamishinan harkokin ma’aikata da kuɗi a hukumar, Nura Hassan Yakasai, ya ce sun zauna sun tsara tsara yadda hukumar za ta biya sauran kuɗaɗen.
Ya ce ba dukkan kamfanonin jirage ne suka nemi ƙarin kudin ba, inda ya ce waɗanda suke SAUDIYYA su ba su nemi wani ƙari ba sai jiragen cikin gida kamar Max-Air da Air-Piece da Azman Air da kuma sauransu.
Batun ƙarin kuɗin ya taso ne a kwanakin baya, bayan da kamfanonin jirage saman na ƙasar suka ƙara dala 250 a kan kuɗin aikin hajjin bana.
NAHCON ta ce za a fara aikin jigilar maniyyata zuwa ƙasa mai tsarki daga ranar Alhamis 25 ga watan Mayu.