Kamfanin mai na Najeriya NNPC ya lashi aniyar cigaba da laluben danyen man fetur a yankin tafkin Chadi.
Kanfanin zai koma Maidugurin ne a cikin mako mai zuwa bayan shekaru 5 da dakatar da aikin sakamakon mummunan ayyukan kungiyoyin ‘yan ta’adda.
Malam Mele Kyari shugaban kamfanin na NNPC, ya bayyana cewa matakin komawa ci gaba da laluben man a jihar Borno wani umarni daga shugaban ƙasa mai barin gado Muhammadu Buhari.
Wannan yunƙuri dai na zuwa ne bayan gano danyen man fetur da aka yi a jihohin Gombe da Bauchi a watan Nuwamba da jihar Nassarawa.
Wannan dalili ya haifar da ɗaura aniyar ganin an cigaba da laluben man da ke jihar Borno cikin kalaman na Mele Kyari.
Don haka, ya tabbatar da cewa, Ma’aikatar za ta tabbatar da samar da tsaro ga ma’aikatanta da za su yi aiki a yankin tafkin Chadi.