• Home  
  • Obama Ya Caccaki Salon Mulkin Trump A Amurka
- Babban Labari - Labarai

Obama Ya Caccaki Salon Mulkin Trump A Amurka

Tsohon shugaban Amurka Barrack Obama ya caccaki gwamnatin Donald Trump a taron gaggamin siyasa na yantakarar gwamna a Virginia da New Jersy. Ya bukaci masu kada kuri’a a zabuka masu zuwa da su yi watsi da abin da ya kira rashin bin doka da sakaci da hauka da ake yi a fadar White House. Obama […]

Tsohon shugaban Amurka Barrack Obama ya caccaki gwamnatin Donald Trump a taron gaggamin siyasa na yantakarar gwamna a Virginia da New Jersy.

Ya bukaci masu kada kuri’a a zabuka masu zuwa da su yi watsi da abin da ya kira rashin bin doka da sakaci da hauka da ake yi a fadar White House.

Obama ya shaida wa Amurkawa cewa Trump da ‘yan Republicans na son su yi tunani domin wasu tsiraru ne kawai a mulki ke daukar mataki amma kuma a bar ‘yan kasa da wahala.

Mista Obama ya yi jan kunne ga ‘yan Republican kan gazawarsu na taka wa Shugaba Trump burki Obama, ba kasafai yake tsoma baki a harkokin siyasa ba amma har yanzu yana da farin jini a tsakanin ‘yan Democrat.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai