Osimhen Ya Lashe Kyautar Gwarzon Ɗan Wasan Bana Na Turkiyya

Ɗan wasan gaban Ƙungiyyar Ƙwallon Ƙafa ta Galatasaray ɗan asalin Najeriya, Victor Osimhen ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasa na bana, a bikin bayar da kyaututtuka ta GQ Türkiye na maza na 2025.

Ɗan wasan mai shekara 26 ya sami kyautar mafi girma a bikin da aka gudanar mai ban sha’awa.

Ya sami kyautar ne saboda rawar da ya taka a Galatasaray a kakar wasa ta bara, inda ya zura ƙwallaye 37 kuma ya taimaka wajen zura ƙwallo sau bakwai a wasanni 41, wanda hakan ya sa Galatasaray ta lashe gasar Turkiya.

Osimhen ya karya tarihin Galatasaray na zama ɗan wasan da ya fi tsada a tarihin Ƙungiyar bayan ya koma akan kuɗi Yuro miliyan 75 daga Napoli.

Osimhen ya ci gaba da yin abin a yaba a wannan kakar, inda ya riga ya zura ƙwallaye 11 a wasanni 14 da ya bugawa ƙungiyar da ke birnin Istanbul.

Galatasaray na matsayi na ɗaya akan teburin babbar gasar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Turkiyya da maki 36 a wasanni 15 da ta buga yayin da Trabzonspor ke matsayi na biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *