• Home  
  • PDP ce za ta lashe zaɓen 2027 a Jigawa — Sule Lamido
- Babban Labari

PDP ce za ta lashe zaɓen 2027 a Jigawa — Sule Lamido

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana ƙwarin gwiwarsa cewa jam’iyyar PDP za ta lashe zaɓen 2027 a jihar. Lamido ya bayyana haka ne a ranar Juma’a, yayin bikin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen PDP a Jigawa, wanda aka gudanar a sakatariyar jam’iyyar da ke Dutse, babban birnin jihar. Taron ya samu halartar […]

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana ƙwarin gwiwarsa cewa jam’iyyar PDP za ta lashe zaɓen 2027 a jihar.

Lamido ya bayyana haka ne a ranar Juma’a, yayin bikin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen PDP a Jigawa, wanda aka gudanar a sakatariyar jam’iyyar da ke Dutse, babban birnin jihar.

Taron ya samu halartar shugabannin jam’iyyar, mambobi da magoya baya, waɗanda suka taru domin nuna goyon bayansu ga PDP gabanin zaɓen 2027.

A jawabinsa, Lamido ya ce PDP ta taka muhimmiyar rawa a siyasar Najeriya, inda ya bayyana cewa wasu daga cikin waɗanda suka kafa APC da sauran jam’iyyu daga PDP suka fito.

Ya ce rikicin da ke addabar APC zai iya zama wata dama ga PDP ta sake samun karɓuwa a wajen jama’a.

Tsohon gwamnan ya kuma ce PDP za ta yi ƙoƙarin magance matsalolin da suka shafi tsadar rayuwa da sauran ƙalubalen da ya danganta da mulkin APC.

Ya buƙaci shugabannin PDP da mambobinta su ƙarfafa jam’iyyar tare da gabatar wa jama’a da manufofi da tsare-tsaren da za su taimaka wajen magance matsalolinsu.

Da yake jawabi a wajen taron, shugaban PDP na Jihar Jigawa, Farfesa Babandi Ibrahim Gumel, ya ce ƙaddamar da kwamitin wani mataki ne na shirya jam’iyyar domin tunkarar zaɓen 2027.

Gumel, ya bayyana cewa PDP za ta zagaya sassa daban-daban na jihar domin ganawa da jama’a tare da sauraron matsalolinsu da kuma neman goyon bayansu.

Ya ce jam’iyyar za ta ƙara mayar da hankali kan ayyukanta a matakin ƙasa, musamman ta hanyar kai saƙonta zuwa ƙauyuka da birane domin wayar da kan masu zaɓe game da manufofinta.

Shugaban na PDP, ya kuma jaddada cewa jam’iyyar za ta gudanar da yaƙin neman zaɓenta cikin lumana, tare da guje wa duk wani abu da zai iya jawo rikicin siyasa.

Ya yi kira ga mambobi da magoya bayan jam’iyyar da su bi doka da oda, su mutunta juna, tare da kiyaye zaman lafiya yayin gudanar da harkokin siyasa.

Gumel ya kuma nemi al’ummar Jigawa da su goyi bayan PDP a zaɓen 2027.

Ƙaddamar da kwamitin na zuwa ne yayin da jam’iyyun siyasa ke ƙara shirye-shiryen neman goyon bayan masu zaɓe gabanin babban zaɓen 2027.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai