• Home  
  • PRP ta ce zarge-zargen da ake yi wa Sanata Shehu Buba ƙoƙarin ɓata suna ne
- Siyasa

PRP ta ce zarge-zargen da ake yi wa Sanata Shehu Buba ƙoƙarin ɓata suna ne

Jam’iyyar adawa ta PRP a Najeriya, ta ce zarge-zargen da ake dangantawa da ɗan takararta na gwamnan Bauchi, Sanata Shehu Buba, na alaƙa da ayyukan ƴan bindiga yunƙuri ne na ɓata masa suna. Jam’iyyar ta ce ba ta so yin tsokaci kan zarge-zargen ba, saboda gudun ƙara ba su muhimmanci ko kuma taimaka wa abin […]

Jam’iyyar adawa ta PRP a Najeriya, ta ce zarge-zargen da ake dangantawa da ɗan takararta na gwamnan Bauchi, Sanata Shehu Buba, na alaƙa da ayyukan ƴan bindiga yunƙuri ne na ɓata masa suna.

Jam’iyyar ta ce ba ta so yin tsokaci kan zarge-zargen ba, saboda gudun ƙara ba su muhimmanci ko kuma taimaka wa abin da ta kira wata maƙarƙashiya.

Sai dai PRP ta ce a yanzu dole ta yi magana akai saboda ta gamsu cewa wani akwai wani “mugun nufi” kan ɗantakarar.

A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran Ƙasa na jam’iyyar, Kwamared Muhammed Ishaq, ya fitar, PRP ta ce waɗannan zarge‑zargen “ƙage ne da aka ƙulla domin rage karɓuwar ɗan takararta”, tana mai cewa masu yaɗa su na jin tsoron shaharar Sanata Buba da yiwuwar nasararsa a zaben gwamna.

Jam’iyyar ta ce waɗanda ke da hujjar aikata wani laifi a kan Sanata Buba su gabatar da ita ga hukumomin da abin ya shafa domin su ɗauki matakin da doka ta tanada.

PRP ta ce tana da yaƙini kan Sanata Shehu Buba, wanda ke wakiltar Bauchi a Majalisar Dattawa, kuma ta bayyana shi a matsayin ɗan ƙasa da ya taka rawar gani wajen ƙoƙarin daƙile matsalar tsaro da ta addabi ƙasar.

Jam’iyyar ta ce tana ganin abokan hamayyar Sanata Shehu Buba da masu sukar sa na jin barazana ne saboda yaɗuwar farin jinin da yake da shi, shi ya sa suka koma yaɗa zarge-zargen da ta kira na ƙarya da ɓata suna.

PRP ta tunatar da masu yaɗa irin labari cewa Sashe na 127(c) na Dokar Zaɓe ta 2026 ya haramta wallafa bayanan ƙarya da ke ɓata sunan ɗantakara, tare da tanadin tara ko zaman gidan yari ga masu aikata hakan.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai