Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya kaddamar da rabon kayan tallafin azumin watan Ramadan tare da bai wa ma’aikatan Gidan Gwamnati da sauran ma’aikatan gwamnati su 602 kudin tallafi domin rage musu radadin halin matsin tattalin arziki a lokacin azumi.
A yayin kaddamar da shirin da aka gudanar a harabar Gidan Gwamnatin Jihar da ke Dutse, gwamnan ya kuma bai wa kowane ma’aikaci Naira dubu ashirin (N20,000), wanda jimillar kudin ta haura Naira miliyan 12.
Gwamna Namadi ya bayyana cewa shirin na daga cikin tsare-tsaren gwamnatinsa na kula da jin dadin ma’aikata da marasa karfi, musamman a lokutan ibada irin na watan Ramadan mai alfarma.
Ya ce kayan tallafin da suka hada da shinkafa, taliya da sauran kayan abinci an tanade su ne domin saukaka wa ma’aikata da iyalansu gudanar da azumi cikin kwanciyar hankali.
Gwamnan ya kara da cewa shirin yana da alaka da sauran shirye-shiryen tallafin Ramadan da gwamnati ke aiwatarwa a fadin jihar, ciki har da shirin ciyar da masu azumi da ake gudanarwa a cibiyoyi kusan 640 da ke cikin kananan mazabu 287 na jihar.
A cewarsa, akalla mutum 420 ne ke cin gajiyar abinci a kowace cibiya a kullum, yayin da ake sa ran shirin zai samar da sama da abinci miliyan 80 a tsawon watan azumi.
Namadi ya bayyana cewa baya ga samar da abinci, shirin yana kuma taimakawa wajen bunkasa tattalin arzikin cikin gida ta hanyar samar da ayyukan yi ga kusan mutane 6,000 da suka hada da masu girki, dillalan abinci da masu kula da rabon abincin a fadin jihar.
Ya kuma bayyana cewa gwamnati ta fadada tallafin zuwa makarantun Almajirai da na Tsangaya, inda makarantu 562 a kananan hukumomi 27 za su amfana da tallafin abinci a watan Ramadan.
Gwamnan ya ce watan Ramadan lokaci ne na tausayi, sadaukarwa da kyautatawa, don haka ya zama wajibi gwamnati ta bullo da shirye-shiryen da za su karfafa hadin kai da taimakon juna a tsakanin al’umma.
Ya kara da cewa rabon kayan abinci ga ma’aikata wata alama ce ta yadda gwamnatinsa ke daraja gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban jihar.
Gwamna Namadi ya kuma bukaci al’ummar jihar da su yi koyi da koyarwar addinin Musulunci ta hanyar taimakon juna, tare da yin addu’o’in samun zaman lafiya, hadin kai da ci gaban Jihar Jigawa da kasa baki daya.
Ya bayyana cewa Ma’aikatar Jin Kai da Agajin Gaggawa ce ke jagorantar rabon tallafin tare da hadin gwiwar Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnati domin tabbatar da gaskiya da ingantaccen rabon kayan ga wadanda suka cancanta.
Shi ma da yake jawabi, Kwamishinan Ma’aikatar Jin Kai, Alhaji Auwalu Danladi Sankara, ya yaba wa gwamnan bisa ci gaba da fadada shirye-shiryen tallafin Ramadan a jihar.
Sankara ya ce adadin masu cin gajiyar shirin ciyar da azumi ya karu sosai a wannan gwamnati, inda ya tashi daga kusan mutum miliyan shida zuwa sama da miliyan takwas.
Ya ce fadada rabon tallafi a duk shekara na nuna kudirin gwamnati na tabbatar da cewa babu wani dan jihar da zai shiga watan Ramadan cikin yunwa.
Wasu daga cikin ma’aikatan da suka amfana sun gode wa Gwamna Namadi kan tallafin, inda suka bayyana shi a matsayin wanda ya zo a kan lokaci duba da halin tsadar rayuwa da ake ciki.
Sun ce kayan abinci da kudin da aka ba su zai taimaka matuka wajen rage musu nauyin kula da iyalansu a watan azumi, tare da yi wa gwamnan addu’ar samun lafiya da nasara domin ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen al’umma.
Hakazalika, ma’aikatan sun yi alkawarin kara himma wajen gudanar da ayyukansu, suna masu cewa irin wannan kulawa daga gwamnati na kara musu kwarin gwiwar yin aiki tukuru.
Rabon tallafin Ramadan na daga cikin manyan tsare-tsaren kariyar jin dadin al’umma da gwamnatin Jihar Jigawa ke aiwatarwa domin inganta rayuwar jama’a da tabbatar da shugabanci mai anfani ga kowa.

