Gwamnatin Tarayyar Najeriya na nazarin wani sabon tsari da zai bai wa ƴan jarida damar yin rakiya ga dakarun sojin ƙasar a lokacin da za su ƙaddamar da wasu farmaki na musamman.
Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, Ministan Tsaro, Christopher Musa ne ya faɗi hakan a yayin wani taro kan tsaro da Ƙungiyar Ƴan Jarida ta Najeriya, ta shirya a Abuja.
Ministan ya ce hakan zai inganta yadda ƴan jarida ke bayar da rahotanni kan haƙiƙanin abin da ke faruwa a yaƙin da ake yi da masu tayar da ƙayar baya da sauran matsalolin tsaron cikin gida.
Ya ce matakin zai ƙara fahimtar da jama’a ayyukan da sojin ƙasar ke yi, kamar yadda mai ba shi shawara na musamman da ya wakilce shi a wajen taron Rear Admiral Olusanya Bankole, ya sanar.
“Ma’aikatar Tsaro na nazarin yadda za a haɗa ƴan jarida da rundunonin soja yayin wasu ayyuka domin su samu damar bayar da sahihan rahotanni tare da fahimtar da jama’a haƙiƙanin ayyukan da ake gudanarwa,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa wannan na daga cikin matakan da ma’aikatar ke ɗauka domin ƙarfafa alaƙa da kafafen yaɗa labarai da kuma tabbatar da cewa bayanan da suka shafi ayyukan soja suna isa ga jama’a cikin sahihanci.
