• Home  
  • Rundunar Yan Sandan Kano Ta Bayyana Nasarori Tare Da Kama Mutane 107 A Shirin Ta Na Operation Kukan Kura
- Babban Labari - Labarai

Rundunar Yan Sandan Kano Ta Bayyana Nasarori Tare Da Kama Mutane 107 A Shirin Ta Na Operation Kukan Kura

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta bayyana gagarumar nasarar data samu, na kama wadanda ake zargi da aikata laifuka mabambanta su 107 a fadin kananan hukumomin jihar 44. Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu bakori, ne ya bayyana hakan lokacin da yake yi wa manema labarai Karin haske a shelkwatar rundunar dake unguwar […]

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta bayyana gagarumar nasarar data samu, na kama wadanda ake zargi da aikata laifuka mabambanta su 107 a fadin kananan hukumomin jihar 44.

Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu bakori, ne ya bayyana hakan lokacin da yake yi wa manema labarai Karin haske a shelkwatar rundunar dake unguwar Bompai, a ranar Litinin.

CP Bakori , ya  ce kamar yadda babban sufeton yan sandan Nijeriya, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, ya bayar da umarni don yin aiki kafada da kafada da al’umma da kuma kawo sabbin tsare-tsaredon magance aikata laifuka rundunar jihar Kano ta kara kaimi wajen kaddamar da Opertion Kukan Kura.

Ya kara da cewa kaddamar da , Opertion Kukan Kura, ya taka rawar gani wurin magance aikata laifuka, musamman harkokin da suka shafi fadan daba a fadin jihar.

Kwamishinan yan sandan ya ce raguwar aikata laifuka  da aka samu ya tabbatar da ingancin tsarin da kuma hadin kai da gudunmawar da al’umma suke bayarwa wajen aiwatar dashi.

A watan augustan 2025 rundunar ta kama mutane 107 bisa zargin aikata laifukan , fashi da makami, safarar miyagun

Wadanda aka kama sun hada da yan fashi da makami 8, masu garkuwa da mutane 8, masu fataucin mutane 3, masu fataucin miyagun kwayoyi 14, Barayin motoci da Babura 8 da Yan Daba 61 da kuma sauran barayi 5.

Kayyakin da aka kwato sun hada da Bindigar kirar AK-47 guda 1 , bindiga kirar gida 7, harsasai guda 11, motoci 8, Babura 8, Shanu 8, Adduna 102, Wukake 74, Sinkin tabar wiwi 111 da kuma kulli-kulli 458 Sannan an tsaratar da mutum daya a hannun masu safarar mutane.

Sauran kayan sun hada da robobin sholisho 211, kwalaben sukudayin 257, kwayar Exol Fatiki 5, kwayar Diazapam Fakiti 20, Shaddar Kampala 44, wayoyin 59, POS guda  3  da katin cire kudi 17 da dai sauransu.

CP Bakori ya ce daga kaddamar da tsarin Opertion Kukan Kura, a ranar 1 ga watan Yuli 2025, zuwa yanzu an kwato muggan makamai 473 da kum miyagun kwayoyi masu yawa.

Haka zalika ya godewa al’ummar jihar Kano musamman wajen bayar da hadin kai da suke yi da hakan ke wajen samun bayanan sirri na tabbatar da tsaro da zaman Lafiya.

A karshe ya yi  kira ga dukkan al’ummar jihar Kano da su ci gaba da ba wa yan sanda hadin kai, su zama masu kula, kuma su ci gaba da kai rahoto akan duk wani abin zargi ga ofishin yan sanda mafi kusa ko ta lambobin waya da suke bayarwa.

   

 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai