• Home  
  • Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Amince Da Karin Naira Biliyan 215.3 A kasafin Kudin 2025
- Babban Labari - Labarai

Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Amince Da Karin Naira Biliyan 215.3 A kasafin Kudin 2025

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da ƙwarya-ƙwaryan kasafin kuɗi na naira biliyan 215.3 bayan tattaunawar da ƴan majalisar suka gudanar a zaman majalisa na yau Litinin. Wannan amincewa ta biyo bayan buƙatar da Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya aika, inda Kakakin majalisar, Jibril Ismail Falgore, ya jagoranci zaman. A wata sanarwa da […]

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da ƙwarya-ƙwaryan kasafin kuɗi na naira biliyan 215.3 bayan tattaunawar da ƴan majalisar suka gudanar a zaman majalisa na yau Litinin.

Wannan amincewa ta biyo bayan buƙatar da Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya aika, inda Kakakin majalisar, Jibril Ismail Falgore, ya jagoranci zaman.

A wata sanarwa da mai magana da yawun majalissar , Kamaluddeen Sani Shawai, ya fitar a ranar Litinin, an bayyana cewa jimillar kuɗin ƙarin kasafin ya kai ₦215,378,374,543.62.

Kakakin ya tabbatar da cewa ‘yan majalisa za su sa ido sosai wajen aiwatar da kasafin, tare da tabbatar da cewa kuɗaɗen da aka ware wa ma’aikatu da hukumomi za a yi amfani da su ta hanyar da ta dace.

Majalisar ta amince da kudirin bayan doguwar muhawara da kuma duba cikakken bayani daga mambobi kafin ƙarshe ta zartar da shi a matsayin doka.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai