An yi kira ga al’umma da su rika kirkiro da sabbin hanyoyi wajen samun sassauci game da matsin rayuwa.
Wannan kiran ya futo ne daga bakin mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayin da aka gudanar da hawan Nasarawa a wannan rana.
Sarkin dai ya samu tarbar Muƙaddashin gwamnan jihar Kano, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da sauran muƙaraban gwamnatin tare da nuna jin daɗinsa game da yadda hawan sallar ke gudana.