A cikin wani saƙon taya murna na bukin Easter da Sarkin Musulmi ya aika wa shugaban Ƙungiyar Kiristocin Najeriya, Daniel Okoh, ya ce rashin fahimta tsakanin addinan biyu, a matsayin ‘aikin Shaiɗan ne,’ kamar yadda Alƙur’ani ya bayyana.
A cikin jawabin nasa, wanda ya samu sa hannun Mataimakin shugaban Majalisar Ƙolin Lura da Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya, Farfesa Salisu Shehu, Sarkin Musulmin ya buƙaci shugaban na CAN da ya haɗa hannu da Masarautar wajen ganin an rage yadda limamai da fastoci ke cusa wa mabiyansu ƙiyayya ta siyasa da kuma munanan kalamai.
Daga ƙarshe mai alfarma Sarkin Musulmi ya taya al’ummar Kirista murnar zagayowar ranar Easter tare da addu’ar samun cigaban Najeriya.