Ɗan majalisar dattijai mai wakiltar mazabar Kudancin Borno, Muhammad Ali Ndume, ya yi karin haske a kan nasarar da Godswill Akpabio ya samu, inda ya ce shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne ya taimaka masa wajan samun nasarar ɗare kujerar shugabancin majalisar.
A hirarsa da manema labarai a jiya talata, Sanatan ya ce, Shugaban kasa ya ziyarci wasu Sanatoci, kuma ya shawo kan su marawa Sanata Akpabio baya ya jagorance su.
Ndume ya kuma shaida cewa sabon shugaban majalisar dattawa ya cancanci wannan kujera.
Majiyarmu ta rewaito Ndume ya na cewa, a zaben 2019 da ya nemi takarar wannan kujera, bai kai ko ina ba domin jam’iyya tagoyi bayan Ahmad Lawan.
Yakara da cewar, abin da ya faru kenan a wannan karo, yanzu kuma APC ta goyi bayan Sanata Akpabio a kan Abdulaziz Yari.
A cikin hirar da akai da shi a gidan talabijin, Sanatan na APC bai kama sunayen wadanda Bola Tinubu ya roka su goyi bayan Akpabio ɗin ba.