A karon farko da ƙasar Turkiya ke zuwa zagaye na biyu a zaben shugaban kasa, bayan da shugaba Erdogan ya gaza kawo kashi 50 na kuri’un da aka kada makwanni 2 da suka gabata, duk da cewa shi ke da mafi yawan kuri’un da aka kada a tsakanin ‘yan takarar na wancan lokaci.
Sai ga shi Erdogan ya sake samun nasara na zama shugaban ƙasar nan Turkiyya.
Tuni dai shuwagabannin duniya suka fara turo da saƙon taya murna ga Erdogan, inda Shugabannin farko-farko da suka aikewa Erdogan sakon taya murna akwai Vladimir Putin na ƙasar Rasha da ke matsayin abokin shugaban Turkiya wanda ya bayyana nasararsa a matsayin tagomashin jajircewarsa ga al’ummarsa,
Sai Joe Biden na Amurka wanda ya yi fatan aiki tare da Erdogan ba tare da ambato takun-sakar da ke tsakaninsu ba a baya-bayan nan game da kungiyar tsaro ta NATO ba.
Nasarar ta Erdogan dai na nuna cewa jagoran mai shekaru 69 zai ci gaba da jan ragamar Turkiyya har zuwa shekarar 2028 inda cikin jawabinsa na farko bayan sanar da sakamakon zaben, shugaban wanda ya shafe shekaru 20 yana mulkar kasar ya yi fatan aiki tare da bangarorin adawa don sake daga likafar kasar.