Shugaban Hukumar Aikin Hajji Na Kasa ya yi murabus

Shugubaban Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) Farfesa Abdullahi Usman Saleh, ya yi murabus daga kujerarsa.

A daren Litinin din nan Aminiya ta samu labarin ajiye mukamin Farfesa Abdullahi Usman Saleh, a daidai da hukumar ke tsaka da shirin gudanar da aikin Hajji na wannan shekarar.

Wani jami’i a hukumar ya bayyana cewa ajiye aikin na da nasaba da takardar korafi da Majalisar Kwamishinoni na Kasa na Hukumar NAHCON suka aike wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu kan zargin Farfesa Abdullahi da aikata ba daidai ba.

Jami’in ya ce, “Takardar korafi da aka aike wa shugaban kasan a kansa ne ya sa shugaban kasa ya tilasta masa ajiye aiki. Kowa ya san yadda takaddama da tabaibaye hukumar tun bayan nadinsa.

Nan gaba ake sa ran Fadar Shugaban Kasa za ta sanar da sunan sabon shugaban hukumar,” in ji jami’in

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *