Farfesa Alkali ya ce ya ajiye muƙamin nasa ne don bai wa wasu sabbin hannu dama, domin ɗorawa kan ci gaban da jam’iyyar ta samu a ɗan taƙaitaccen lokacin da ya yi yana jagorantar ta.
Alƙali ya ce duba da irin abubuwan da suka faru kafin zaɓukan da suka gabata, da abubuwan da da suka faru a lokacin zaɓukan da suka gabata, yana cike da fatan cewa jam’iyyar, na da makoma mai kyau.
Sannan kuma a yace yana cike da fatan jam’iyyar za ta kasance cikin manyan jam’iyyun siyasar ƙasar, da za su iya cin zaɓen shugaban ƙasa da sauran muƙamai a kakar zaɓe ta 2027.
Daga ƙarshe ya miƙa sakon godiyarsa ga jagoran jam’iyyar na ƙasa Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da ɗaukacin mambobin kwamitin amintattu na jam’iyar da sauran zaɓaɓɓun ‘yan siyasa na jam’iyyar bisa damar da ya ce sun ba shi na gudanar da mulkin jam’iyyar cikin kwanciyar hankali
Shugaban jam’iyar NNPP na ƙasa Farfesa Rufai Alkali, ya ajiye muƙaminsa.
Wannan na kunshe cikin wata wasiƙa da ya aike wa sakataren jam’iyyar na ƙasa.