Home » Sojin Najeriya Sun Kashe Wasu ‘Yan Ta’adda 70

Sojin Najeriya Sun Kashe Wasu ‘Yan Ta’adda 70

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment
Sojin Najeriya Sun Kashe Wasu 'Yan Ta'adda 70

Dakarun sojin Najeriya sun kashe mutane sama da 70 da ake zargin ‘yan ta’adda ne a wani farmaki da suka kai a yankin Arewa maso Gabashin kasar.

Daraktan yada labarai na rundunar, Manjo Janar Musa Danmadami, ya bayyana hakan a ranar Alhamis, yayin da yake yi wa manema labarai karin haske game da ayyukan da sojojin suka yi cikin makonni biyu da suka wuce.

Ya ce an kuma kama ‘yan ta’adda sama da 140 a tsawon lokacin, tare da kwato makamai da dama da suka hada da bama bamai hadin gida.

A halin da ake ciki kuma, rundunar sojin ta kuma tababtar da cewa an kubutar da biyu daga cikin ‘yan matan makarantar Chibok da aka sace a watan Afrilun 2014, baya ga wasu fararen hula sama da 150 da aka ceto a wasu hare-haren da sojoji suka kai a yankin arewa maso gabas.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?