Babban Labari
Tinubu ya yi alhinin rasuwar Bamanga Tukur
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana alhininsa kan rasuwar fitaccen ɗan kasuwa kuma tsohon gwamnan tsohuwar Jihar Gongola, Alhaji Bamanga Muhammad Tukur, wanda ya rasu yana da shekara 90 a duniya. A cikin saƙon ta’aziyyarsa, Shugaba Tinubu ya bayyana rasuwar Alhaji Bamanga Tukur, wanda ke riƙe da sarautar Tafidan Adamawa, a matsayin wani giɓi […]
