Wasu matasa sun bankawa ɓarawon waya wuta a Ɗorayi
Wasu matasa a unguwar Dorayi dake jihar Kano sun bankawa wani da ake zargin barawon waya ne wuta, bayan da kwace wayar wata mata. Rahotanni sun ce barawon ya chakawa matar wuka a kirjin ta kafin matasan su hallaka shi ta hanyar kone shi da taya. Tuni aka garzaya da matar zuwa asibiti cikin mummunan yanayi […]