Wasu matasa sun bankawa ɓarawon waya wuta a Ɗorayi

Wasu matasa a unguwar Dorayi dake jihar Kano sun bankawa wani da ake zargin barawon waya ne wuta, bayan da kwace wayar wata mata.

Rahotanni sun ce barawon ya chakawa matar wuka a kirjin ta kafin matasan su hallaka shi ta hanyar kone shi da taya.

Tuni aka garzaya da matar zuwa asibiti cikin mummunan yanayi domin samun kulawar gaggawa daga likitoci, ya yin da jami’an tsaro suka iso wurin suka dauki konanniyar gawar barawon, don gudanar da bincike.

Har zuwa wannan lokaci rundunar yan sandan jihar Kano, bata fitar da wata sanarwa ba kan faruwar lamarin.

Post masu alaƙa

2027: ADC ta zargi Kwankwaso da yi wa Tinubu aiki

PDP ce za ta lashe zaɓen 2027 a Jigawa — Sule Lamido

Zaɓen 2027: Rundunar yan sanda jihar Kano ta ba da tabbacin tsaro,tare da yin gargaɗi kan yada labaran ƙarya