Kotu ta tura tsohon ministan ƙwadago Chris Ngige gidan yari
Wata babbar kotun tarayya mai zamanta a garin Gwarimpa da ke babban birnin tarayya Abuja ta tura tsohon ministan ƙwadago Chris Ngige a gidan yarin Kuje. Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ce ta gurfanar da tsohon ministan a gaban mai shari’a Mariam Hassan bisa tuhume-tuhume guda takwas da suka danganci cin hanci […]