Hukumar Civil Defense Zata yi bincike kan zargin mutawar matashi a ofishinta dake Kano.
Rundunar tsaro ta Civil Defense reshen jihar Kano, ta ce, za ta yi ƙwaƙƙwaran bincike kan zargin kashe wani matashi mai suna, Halifa Abdullahi, a ofishin rundunar na ƙaramar hukumar Fagge. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SC Ibrahim Idris Abdullahi, ne ya bayyana hakan, a ranar Alhamis, biyo bayan yadda a ka zargi jami’an […]