Hukumar Civil Defense Zata yi bincike kan zargin mutawar matashi a ofishinta dake Kano.

Rundunar tsaro ta Civil Defense reshen jihar Kano, ta ce, za ta yi ƙwaƙƙwaran bincike kan zargin kashe wani matashi mai suna, Halifa Abdullahi, a ofishin rundunar na ƙaramar hukumar Fagge.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SC Ibrahim Idris Abdullahi, ne ya bayyana hakan, a ranar Alhamis, biyo bayan yadda a ka zargi jami’an rundunar a ofishin na Fagge da sanadiyyar rasuwar matashin da ke taimaka musu a jiya Laraba 8 ga Janairu, 2026.

SC Ibrahim Idris, ya ce, yanzu haka shugaban rundunar ya kafa wani kwamiti, domin gudanar da bincike, domin tabbatar da adalci a kan al’amarin.

Ya kuma ce, kwamitin da aka kafa zai yi aiki ne tare da rundunar ƴan sandan jihar Kano, domin ganin an zurfafa bincike tare da ɗaukar matakin da ya dace a kan al’amarin.

Post masu alaƙa

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wanda ake zargi da garkuwa da mutane,sannan an kwato Drone.

Ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi ta buƙaci a biya diyyar masu haƙar ma’adinai 37 da suka rasu Neja

Atiku ya buƙaci Tinubu ya yi bayanin dalilinsa na ƙin halartar taron UNGA karo na uku a jere