Babban Labari
Mutanen gari sun fatattaki ’yan bindiga tare da kashe 4 daga cikinsu a Katsina
Mazauna ƙauyen Dansarai da ke Ƙaramar Hukumar Malumfashi a Jihar Katsina, sun yi artabu da ’yan bindigar da suka kai musu hari a ranar Talata, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa. A cewar mazauna yankin, ’yan bindigar sun shiga ƙauyen ne a kan babura ɗauke da bindigogi ƙirar AK-47, inda suka riƙa harbe-harbe kan […]

