Matasan Arewa sun bukaci gwamnonin arewa maso gabas su fi bai wa tsaro da samar da aikin yi muhimmanci
Kungiyoyin matasa a arewacin Nijeriya sun bayyana damuwarsu kan yadda wasu shugabanni ke bai wa wasu ayyuka fifiko, maimakon mayar da hankali wajen magance matsalolin da suka addabi al’ummar yankin. Wannan na zuwa ne bayan da gwamnonin jihohin Arewa maso Gabashin Nijeriya suka bayyana shirin kafa kamfanin jiragen sama domin zirga-zirga tsakanin jihohin shida da […]