Kungiyoyin matasa a arewacin Nijeriya sun bayyana damuwarsu kan yadda wasu shugabanni ke bai wa wasu ayyuka fifiko, maimakon mayar da hankali wajen magance matsalolin da suka addabi al’ummar yankin.
Wannan na zuwa ne bayan da gwamnonin jihohin Arewa maso Gabashin Nijeriya suka bayyana shirin kafa kamfanin jiragen sama domin zirga-zirga tsakanin jihohin shida da ke yankin.
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya ce an ware sama da naira biliyan 15 a matsayin gudunmawar fara aikin.
Da yake tsokaci kan wannan shiri, Ambasada Zaidu Ayuba Alhaji, jagoran Majalisar Tuntuba ta Matasan Arewa, ya ce kamata ya yi gwamnonin su fara mayar da hankali wajen daukar matakan da za su magance matsalar tsaro da ta addabi yankin.
A cewarsa, kafin a samu ingantaccen zirga-zirgar jiragen sama, akwai bukatar a samar da yanayin tsaro da kwanciyar hankali, musamman ganin yadda matsalar tsaro ta shafi rayuwar jama’a da harkokin tattalin arziki a yankin.
Sai dai Ambasada Zaidu ya kuma bayyana cewa, ta wata mahanga, kafa kamfanin jiragen saman na iya taimakawa wajen bunkasa tattalin arzikin Arewa maso Gabas, tare da inganta zirga-zirga da hulda tsakanin jihohin yankin.
A karshe, ya yi kira ga gwamnonin da su kara mayar da hankali wajen samar da cibiyoyin koyar da matasa sana’o’i domin samar da guraben aikin yi, da kuma rage matsalolin rashin aikin yi da talauci da ke addabar al’ummar yankin.