Gobara

Gobara ta sake tashi a wata kasuwa a Kano

Wata gobara da ta tashi da asuba ta lalata akalla shaguna 50 a kasuwar Fatima Simra Multi-Purpose Market da ke unguwar Dakata a Jihar Kano. Shugaban kwamitin kashe gobarar kasuwar, Dauda Haruna Chula, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce gobarar ta fara ne misalin ƙarfe 4 na asubahin ranar Juma’a. Ya bayyana cewa […]

Read more

Gobara ta tashi a Kasuwar Singa da ke Kano

Gobara ta tashi a Kasuwar Singa da ke birnin Kano a safiyar Litinin ɗin nan. Rahotanni sun nuna cewa ’yan kasuwa da mazauna sun shiga tashin hankali matuƙa sakamakon tashin gobarar a shahararriyar kasuwar kayan abincin kwali da da ke titin Bello Road. ‎An yi asarar dukiyoyi na maƙudan kuɗaɗe a sanadiyyar gobarar ta safiyar […]

Read more

Gobara ta cinye shaguna 50 a Tsohuwar Kasuwar Sokoto

Wutar gobara da ta tashi a safiyar Lahadi a sanadin wutar lantarki ta laƙume shaguna 50 a tsohuwar Kasuwar Sakkwato. Wutar ta kama a layi mafi tsada a kasuwar inda ake sayar da kayan tireda da harkar canjin kuɗi da turare da sauran kayan abinci na kwali, inda ta cinye kayan miliyoyin naira wanda har […]

Read more

Mutane 20 Sun Rasu Sakamakon Gobara A Indonesia

Wata gobara da ta tashi a wani gini mai tsawo a babban birnin Indonesia, ta yi ajalin mutum aƙalla ashirin. Shugaban yansandan Jakarta ya ce masu kashe gobara na ci gaba da duba ginin ko akwai sauran mutanen da ke makale a ciki. Wakiliyar BBC ta ruwaito cewa hukumomi sun ce da alama gobarar ta […]

Read more

Fashewar Tankar Mai Ta Yi Ajalin Mutane 30 A Neja

Ana fargabar cewa aƙalla mutum 30 sun riga mu gidan gaskiya sakamakon fashewar wata tankar man fetur a ƙauyen Essa da ke hanyar Agaei zuwa Bida a ƙaramar hukumar Katcha ta Jihar Neja. Aminiya ta ruwaito cewa, akwai kuma kimanin mutum 40 da suka jikkata wadanda su ma suka rububin kwalfar man fetur bayan kifewar […]

Read more

Gobarar Daji Da Iska Mai Ƙarfi Sun Afkawa Isra’ila

Wata gobara mai karfin gaske da iska sun afkawa dazukan kasar Isra’ila, inda aka ce al’amarin na cigaba da tsananta daga daren jiya Laraba zuwa wayewar yau Alhamis, abin da ya tilastawa Firaminista Benjamin Netanyahu sanar da dokar ta ɓaci tare da neman agajin ƙasashen duniya don murƙushe wutar wadda ta durfafi dazukan da ke gab da shiga birnin Ƙudus. 

Read more