Fashewar Tankar Mai Ta Yi Ajalin Mutane 30 A Neja

Ana fargabar cewa aƙalla mutum 30 sun riga mu gidan gaskiya sakamakon fashewar wata tankar man fetur a ƙauyen Essa da ke hanyar Agaei zuwa Bida a ƙaramar hukumar Katcha ta Jihar Neja.

Aminiya ta ruwaito cewa, akwai kuma kimanin mutum 40 da suka jikkata wadanda su ma suka rububin kwalfar man fetur bayan kifewar tankar.

Tun da misalin karfe 11 na safiyar wannan Talatar ce tankar ta kife a titin Essan da aka bayyana cewa lalacewar hanyar ce ta haddasa hatsarin.

Daraktan Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Abdullahi Baba Arah, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

“Gaskiya ne, tankar ta faɗi a ƙauyen Essa. Ma’aikatanmu sun ziyarci wurin domin aikin ceto.

“Zuwa yanzu an tabbatar mutum 24 sun mutu, yayin da 40 suka samu munanan raunuka kuma an garzaya da su Asibitin Tarayya, Bida,” in ji shi.

Shi ma Shugaban Ƙungiyar Direbobin Tankuna ta Jihar Neja, Kwamared Farouk Mohammed Kawo, ya tabbatar da faruwar hatsarin, yana mai cewa tankar wadda ta faɗi ta kama da wuta, ta taso ne daga Legas zuwa Arewa.

Kwamared Kawo ya koka da cewa a wannan watan kaɗai, tankuna fiye da 30 sun yi haɗari a hanyar saboda lalacewar titin, yana mai roƙon Gwamna Mohammed Umar Bago, da ya gaggauta gyaran hanyar don rage asarar rayuka da dukiyoyi.

Post masu alaƙa

An kashe kwamandojin ’yan bindiga biyu a Katsina

NAPTIP ta ceto sama da yara 180 da ake safararsu ta hanyar ƙungiyoyin fara hula na bogi

Nafi’u ya gargaɗi Atiku ya daina sukar Tinubu da sunan ADC