Gobara ta ƙone dukiyar N15m a Gusau
Gobara ta ƙone dukiya ta kimanin Naira miliyan 15 wadda ta tashi a wata ma’adanar kayan ado da ke unguwar Barakallahu a birnin Gusau na Jihar Zamfara. Wani ganau, Sambo Balarabe, ya ce gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 8 na dare, bayan wani direban babur da ke wucewa ya hango hayaƙi na tashi […]