Gobara ta ƙone dukiyar N15m a Gusau

Gobara ta ƙone dukiya ta kimanin Naira miliyan 15 wadda ta tashi a wata ma’adanar kayan ado da ke unguwar Barakallahu a birnin Gusau na Jihar Zamfara.

Wani ganau, Sambo Balarabe, ya ce gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 8 na dare, bayan wani direban babur da ke wucewa ya hango hayaƙi na tashi daga saman rufin ma’ajiyar, inda nan take ya ankarar da jama’a.

Ya ce an yi gaggawar kiran jami’an hukumar kashe gobara waɗanda suka isa wajen tun kafin isowar mai ma’adanar kayayyakin

Kazalika, Sambo ya ce mutane sun taimaka wajen buɗe ma’ajiyar domin bai wa jami’an damar shiga.

Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Zamfara, Abdullahi Jibo, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa, inda ya ce ma’ajiyar kayayyakin mallakar wata mata ce mai suna Shafa’atu Sulaiman da ke kusa da Sakandiren Command a Gusau.

Sanarwar ta ce bincike ya nuna cewa wutar lantarki ce ta haddasa gobarar wadda aka yi sa’a ba a samu asarar rai ko rauni ba.

Sai dai darektan ya ce dukkan kayayyakin da ke cikin ma’ajiyar sun lalace gaba ɗaya waɗanda aka kiyasta asarar da Naira miliyan 15.

Post masu alaƙa

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wanda ake zargi da garkuwa da mutane,sannan an kwato Drone.

Ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi ta buƙaci a biya diyyar masu haƙar ma’adinai 37 da suka rasu Neja

Atiku ya buƙaci Tinubu ya yi bayanin dalilinsa na ƙin halartar taron UNGA karo na uku a jere