Za a yi bincike kan zargin kisan Dadiyata da wasu mutane 5 a Kano- IGP Olatunji Disu.
Fitaccen lauya mai fafutukar kare haƙƙin bil’adama, Barista Nuhu Hamza Dantani, ya gana da babban sufeton ƴan sandan Najeriya, IGP Olayunji Disu, kan zarge-zargen da ake yi wa wasu jami’an ƴan sanda da tauye haƙƙin jama’a. Ɗantani ya bayyana hakan bayan ganawarsa da babban sufeton ƴan sandan Nijeriya, a shafinsa na Facebook a ranar juma’arnan. […]