Fitaccen lauya mai fafutukar kare haƙƙin bil’adama, Barista Nuhu Hamza Dantani, ya gana da babban sufeton ƴan sandan Najeriya, IGP Olayunji Disu, kan zarge-zargen da ake yi wa wasu jami’an ƴan sanda da tauye haƙƙin jama’a.
Ɗantani ya bayyana hakan bayan ganawarsa da babban sufeton ƴan sandan Nijeriya, a shafinsa na Facebook a ranar juma’arnan.
A yayin ganawar ta su, Nuhu Dantani, ya yi zargin cewa wasu ƴan sanda suna tsare mutane ba bisa ƙa’ida ba, ko cin zarafinsu ta hanyar duka da kuma barazana.
Haka kuma sun tattauna kan hanyoyin da za a bi don daƙile matsalar faɗan daba a jihar Kano, da kuma gudanar da bincike kan kisan wasu mutane biyar da aka yi a makonnan.
Anasa ɓangaren babban sufeton ƴan sandan Nijeriya, IGP Olayunji Disu ya tabbatar da cewa rundunar ƴan sandan, za ta ɗauki mataki kan duk jami’in da aka samu da laifin take haƙƙin jama’a, yana mai kira ga manyan jami’an rundunar wajen bin ƙ’’idar tsare mutane.
Haka zalika, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan zargin kashe, wani ɗan gwagwarmaya mai suna Dadiyata.
A ƙarshe, IGP Disu ya buƙaci dukkanin waɗanda suke da ƙorafi a kan jami’an ƴan sanda ko tsare su ba bisa doka ba, da su kai ƙorafinsu ga sashen karɓar ƙorafe-ƙorafe na rundunar, wato CRU, don gudanar da bincike.