Gwamnatin Kamaru Ta Tabbatar Da Mutuwar Mutane 4 A Zanga-zangar Da Ake Ci Gaba Da Yi.
Gwamnatin Kamaru ta tabbatar da cewa mutum hudu suka mutu a zanga-zangar da ƴanƙasar suka gudanar a ranar Lahadi a birnin Doula gabanin sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a yau Litinin. Ɗaruruwan magoya bayan ɗantakarar adawa, Issa Tchiroma Bakari ne suka fito zanga-zangar. Hukumomi sun ce an kai wa ƴansanda da jami’an tsaro hari […]