Gwamnatin Kamaru Ta Tabbatar Da Mutuwar Mutane 4 A Zanga-zangar Da Ake Ci Gaba Da Yi.

Gwamnatin Kamaru ta tabbatar da cewa mutum hudu suka mutu a zanga-zangar da ƴanƙasar suka gudanar a ranar Lahadi a birnin Doula gabanin sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a yau Litinin.

Ɗaruruwan magoya bayan ɗantakarar adawa, Issa Tchiroma Bakari ne suka fito zanga-zangar.

Tchiroma Bakary ya ƙalubalanci shugaba Paul Biya – wanda ya shafe shekara 43 yana shugabanci a ƙasar.

Tuni jagoran adawar ya ayyana cewa shi ne ya yi nasara a zaɓen, duk da cewa a yau Litinin ne ake sa ran sanar da sakamakon a hukumance.

Post masu alaƙa

Kotu ta dage hukunci kan shari’ar datse yatsa bisa alkawarin naira miliyan 80.

Ba za mu dawo da tallafin man fetur ba —Fadar Shugaban Ƙasa

An Kashe Makiyaya 50 An Sace Shanu Sama da Dubu 2 A Kaduna — MACBAN