Matasa sun ƙona motar jami’an KAROTA a Kano
Wasu fusatattun matasa sun ƙona wata motar aiki ta Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) bayan wani hatsari da ya faru a yankin Kwanar Dawaki da ke kan babbar hanyar Kano zuwa Zariya. Matasan sun zargi jami’an KAROTA da haddasa hatsarin, lamarin da ya sa suka banka wa motar hukumar wuta. […]