Matasa sun ƙona motar jami’an KAROTA a Kano

Wasu fusatattun matasa sun ƙona wata motar aiki ta Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) bayan wani hatsari da ya faru a yankin Kwanar Dawaki da ke kan babbar hanyar Kano zuwa Zariya.

Matasan sun zargi jami’an KAROTA da haddasa hatsarin, lamarin da ya sa suka banka wa motar hukumar wuta.

Mataimakin Manajan-Daraktan KAROTA, Auwal Lawal Aranposu, ya shaida wa wakilinmu cewa hatsarin ya rutsa da wata motar ƙirar Sharon da kuma wata tirela, inda babbar motar ta buge motar Sharon, abin da ya sa ta yi ta adungure sau da dama.

A cewarsa, a lokacin da hatsarin ya faru, jami’an KAROTA sun yi ƙoƙarin cafke direban babbar motar, amma ya tsere.

“Nan take wasu da ake zargin ɓata-gari ne suka kai wa jami’anmu hari, saboda suna zaton su ne suka haddasa hatsarin. Daga nan suka ƙona motar aikin hukumar,” in ji Aranposu.

Ya jaddada cewa jami’an KAROTA ba su da hannu a haddasa hatsarin, yana mai cewa maimakon haka, sun taimaka wajen ceto waɗanda abin ya shafa tare da kai su asibiti domin samun kulawar likitoci.

Post masu alaƙa

Rundunar yan sandan jihar Kano tasha alawashin ƙara kaimi wajen yaƙi da daba da fataucin miyagun ƙwayoyi.

Rundunar yan sandan jihar Kano ta gargadi al’umma kan bin dokokin tuki.

Ana zargin mahaifi da kashe ’yarsa kan auren dole a Katsina