Tinubu ya tura Shettima ya wakilci Najeriya a taron Majalisar Ɗinkin Duniya a Amurka
Mataimakin Shugaban Ƙasar Najeriya, Kashim Shettima, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarce shi da jagorantar tawagar Najeriya zuwa babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) karo na 81 da za a yi a birnin New York na ƙasar Amurka. A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Shettima ya bayyana cewa […]