Mataimakin Shugaban Ƙasar Najeriya, Kashim Shettima, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarce shi da jagorantar tawagar Najeriya zuwa babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) karo na 81 da za a yi a birnin New York na ƙasar Amurka.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Shettima ya bayyana cewa tawagar za ta haɗa da Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, da Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, da ministoci da sauran manyan jami’an gwamnati.
An shirya gudanar da muhawarar babban taron na UNGA daga ranar 22 zuwa 28 ga Satumban 2026.
Ana sa ran Najeriya za ta yi amfani da taron wajen bayyana matsayinta kan muhimman batutuwan duniya da suka shafi tsaro, ci gaba da tattalin arziki.