Kotun Ƙoli ta ɗage Shari’ar kujerar Sarkin Kano zuwa 2027
Kotun Ƙoli ta ɗage sauraron ƙarar da aka shigar gabanta kan dambarwar Masarautar Kano da shekara guda. A zamanta na ranar Litinin, 20 ga Afrilu, 2026, kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa zuwa 19 ga watan Afrilu, shekara ta 2027.