Gwamnonin Arewa Sun Yi Allah-Wadai Da Sace Dalibai Mata A Kebbi
Ƙungiyar Gwamnonin Arewa (NGF) ta bayyana matuƙar damuwa kan harin da aka kai Makarantar Sakandiren Mata da ke Maga a ƙaramar hukumar Danko/Wasagu ta Jihar Kebbi, wanda ya yi sanadin sace ɗalibai mata da dama tare da kashe jami’an makarantar. Shugaban ƙungiyar, kuma Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici […]