Gwamnonin Arewa Sun Yi Allah-Wadai Da Sace Dalibai Mata A Kebbi

Ƙungiyar Gwamnonin Arewa (NGF) ta bayyana matuƙar damuwa kan harin da aka kai Makarantar Sakandiren Mata da ke Maga a ƙaramar hukumar Danko/Wasagu ta Jihar Kebbi, wanda ya yi sanadin sace ɗalibai mata da dama tare da kashe jami’an makarantar.

Shugaban ƙungiyar, kuma Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici da rashin hankali, yana mai cewa ci gaba da kai hare-hare kan makarantun Arewa barazana ce ga zaman lafiya da makomar ilimi a yankin.

A madadin sauran gwamnonin Arewa, Gwamna Inuwa ya jajanta wa Gwamnatin Jihar Kebbi, iyalan waɗanda aka sace da kuma waɗanda suka rasa rayukansu, tare da tabbatar wa Gwamna Nasir Idris da cikakkiyar goyon bayan ƙungiyar.

A wata sanarwa da Babban Daraktan Yaɗa Labarai na Gwamnatin Jihar Gombe, Isma’ila Uba Misilli, ya fitar, ƙungiyar ta buƙaci a gaggauta haɗa kai tsakanin jami’an tsaro domin ceto ’yan matan da aka sace da kuma kamo waɗanda suka aikata laifin.

Gwamnonin Arewa sun jaddada aniyarsu ta yin aiki kafada da kafada da Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaron makarantun yankin.

Gwamna Inuwa ya yi addu’ar Allah Ya dawo da ’yan matan lafiya, tare da kira ga al’umma da su kasance masu sa ido da bayar da goyon baya ga jami’an tsaro

Post masu alaƙa

Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kuɗin 2026 na naira tiriliyan 68

Ƙungiyar muhaɗu mugyara ta bayyana Muhasa TVR a matsayin kan gaba wajen gyaran tarbiyyar al’umma.

Fursuna ya tsere bayan hatsarin motar jami’ai a Yobe