Rikice-rikicen Da Ake Yi A Nijar Da Sudan Ne Ke Shafar Najeriya- Burtaniya
Kasar Burtaniya ta bayyana damuwarta kan tabarbarewar tsaro a Najeriya, inda ta bayyana hakan a matsayin “babban abin tada hankali” da ke faruwa sakamon rikice-rikicen da suka ki ci-suka ki cinye wa a jamhuriya Nijar da kuma Kasar Sudan.